Jami’an tsaro na KADVIS sun kama wani matashi da ya addabi masallatai da satar Alkur’ani a yankin Zariya, Jihar Kaduna.
Dubun matashin ta cika ne a masallacin Gamandi Kofar Galadima da ke Zariya inda aka same shi da Alkur’anai tawkas da suma littafin Askari gida guda.
A lokacin da jami’an KADVIS suke tuhumar shi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya dade yana satar littafai a masallatai daban-daban.
Ya kuma shaida musu cewa ya sayar da Alkur’anai akalla 57 ga wani mutum, wanda a halin yanzu ake nema.
- Yaran Arewa masu cutar tamowa sun ƙaru da 51% —Likitoci
- NAJERIYA A YAU: Cire Tallafin Mai Ne Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Kunci?
Bayan titsiye wanda ake zargin, jami’an na KADVIS sun yi nasarar tatsar bayan bayanai kan wanda ke sayen littafan satan a hannunsa.