An gurfanar da wani matashi mai dillancin filaye a Kotun Majistare ta Kaduna kan zargin damfarar wani mutum Naira miliyan 7.9.
A ranar Alhamis kotun ta sami matashin da laifin samun kudi ta hanyar karya da kuma sata.
- Buhari Ya yi tir da kisan Limamin Cocin da ’Yan Bindiga suka sace a Kaduna
- Zargin batanci: Abduljabbar ya nemi a sauya masa kotu
Dan sanda mai tuhuma, Sufeto Chidi Leo, ya fada wa kotun cewa mai kare kansa ya aikata laifin ne tsakanin watan Janairu da Yunin 2021 a Kaduna.
Leo ya yi zargin matashin ya karbi Naira miliyan 7.9 daga hannun mai kara, David Kefas, da sunan zai taimaka masa wajen sayen fili mai girman kadada 10 a unguwar Maraba Rido da ke Kaduna.
“Ya karbi 7.9 daga mai kara da nufin sayar masa da filin amma sai bai yi hakan ba,” inji jami’i mai tuhuma.
Ya kara da cewa, ko da mai kara ya bukaci a mayar masa da kudinsa tun da filin bai samu ba, hakan ya faskara, kuma wanda ake zargin ya tsare.
Ya ce an damke wanda ake zargin ne a Barkin Ladi, Jihar Filato bayan da mai kara ya kai korafinsa ga Sashen Bincikin Manyan Laifuka na ’yan sanda (SCIID).
A cewar mai tuhuma, laifukan sun saba wa sassa na 243 da 217 na ‘Penal Code’ na Jihar Kaduna, 2017.
Kodayake wanda ake zarign ya ki amsa tuhumar da aka masa, amma alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel ya ba da belinsa a kan Naira miliyan daya da kuma shaidu guda biyu.
Sannan ya dage ci gaba da shari’ar 19 ga Agusta mai kamawa.