✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama matashi da laifin yi wa ‘yar shekara 75 fyade a Anambra

Kafin shigarsa hannu tuni wasu fusatattun mutane sun yi masa dukan tsiya.

’Yan sanda sun cafke wani mutum mai suna Sunday Nwadiagba kan zargin yi wa wata tsohuwa mai shekaru 75 fyade a Jihar Anambra. 

Rundunar ’yan sandan bayan ta ceto matashin mai shekaru 30 daga hannun wasu fustattun mutane da suka yi yunkurin daukar doka a hannunsu, ta kuma sakaya shi inda take ci gaba da bincike a kan lamarin.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce an kama Mista Sunday wanda dan asalin Jihar Ebonyi ne yana tsaka da zakke wa dattijuwar a gonarta da ke Nkwelle Awkuzuz a Karamar Hukumar ta Jihar Anambra.

Ya ce kukan tsohuwar da kururuwar neman a kawo mata dauki ne ya ja hankalin masu wucewa, lamarin da ya kai jama’a sun hallara a wurin da yake aika-aikar.

“Sai dai kafin shigarsa hannunmu tuni wasu fusatattun mutane sun yi masa dukan tsiya.

“Hakan ne ya sanya muka mika shi tare da tsohuwar da abin ya shafa zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Echeng Echeng ya gargadi jama’a a kan hatsarin da ke tattare da daukar doka a hannunsu a duk lokacin da suka kama wadanda ake zargi da aikata wani laifi.

Ya yi kashedin cewa jama’a su rika mika duk wani wanda ake zargi da wani laifi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa a duk lokacin da aka kama shi.

Ya ce wannan ita kadai ce hanyar da za ta bai wa ’yan sanda damar gudanar da binciken da ya dace kan laifin wadanda ake zargin; da kuma gurfanar da su a gaban shari’a kamar yadda wasu doka ta tanada.