Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta damke wasu matasa uku da suka yi wata buburwa fyde tare da daukar bidiyon fasadin.
Kakakin Rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce, “Yarinyar ta je wanka ne a rafin Odo-pata da ke garin Pata Abiodun na Karamar Hukumar Ifo, matasan suka ja ta daji suka yi mata fyade daya bayan daya.
- An kama limamai 2 bisa zargin yi wa ’yar bautar kasa fyade
- An kama wanda ya yi wa yarinya fyade har ta mutu
- An tsare magidanci kan zargin yi wa yara 10 fyade
“Daya daga cikinsu ya rika daukar bidiyon lalatar da suke yi da ita, suka kuma yi mata barazanar yada bidiyon a kafafen sadarwa idan ta tona musu asiri,” inji samnarwar da fitar.
Oyeyemi ya ce da ’yan sanda suka samu labari sai DPO na Ifo, CSP Adeniyi Adekunle, ya jagoranci jami’an bincike suka kamo su kuma sun amsa laifi, yarinyar da suka yi wa fyade kuma an kai ta asibiti.
Ya kuma ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Edward Ajogun, ya bayar da umarnin mayar da wadanda ake zargin Sashen Yaki da Safarar bil’Adama da Azabtar da Kananan Rara don yin cikakken bincike kafin a gurfanar da su a gaban kuliya.