Rundunar ’Yan Sandan jihar Kaduna ta ce ta kama wata mata a jihar da ta dauko yara tara a motar daukar kaya, daga karamar hukumar Danbatta da ke Kano, ta nufi jihar Ogun da su.
Yaran dai sun hada da masu shekaru 10 zuwa 15, kuma matar ta nufi garin Ijebu-Ode da je jihar Ogun ne da su, kafin a tare ta a jihar ta Kaduna.
- Bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa tiriliyan N42
- NAJERIYA A YAU: Irin Asarar Da Cin Ganda Ke Janyo Wa Tattalin Arzikin Najeriya
Kakakin rundunar a Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce sun tare motar ce a shingen bincike na Kurmin Mashi, bayan sun lura babu taga ko daya a jikinta, duk da cewa akwai mutane a ciki.
“Da misalin karfe 4:00 na yammacin Lahadi ne jami’anmu suka kama motar.
“Daga matar har yaran ’yan Dambatta ne duka, kuma ta ce ta dauko su ne don taya ta sana’ar siyar da abinci da take yi a jihar Ogun.
“Amma ko hakan ma ta saba wa dokar kasa, saboda karancin shekarunsu,” inji Jalige.
Kakakin ya ce za su ci gaba da bincike kan lamarin, kafin daukar mataki na gaba.