✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu sayar da jabun rigakafin COVID-19

Jami’an tsaro sun kwace jabun rigakafin cutar 3,000 a hannun mutum 80 da aka kama.

Hukumomi a kasar China sun damke gungun masu kerawa da sayar da jabun allurar rigakafin cutar COVID-19 ga kasashen waje.

Akalla mutum 80 masu kerawa da sayar jabun rigakafin a China da wasu kasashe ne jami’an tsaro suka cafke suka kuma kwace magungunan sama da guda 3,000 a hannunsu.

Yayin tabbatar da kama mutanen, Kakain Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar, Wang Wenbin ya ce: “China ta riga ta sanar da kasashen da lamarin ya shafa.”

Kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar China ya ce a ’yan sanda sun kama masu jabun rigakafin ne a biranen Beijing da Jiangsu da Shandong inda suke sarrafa sinadarin Saline suna sayarwa a matsayin rigakafin COVID-19.

Gidan talabijin na Gwamnatin China ya ce tun watan Satumban 2020 gungun mutanen da dubun tasu ta cika ke ta damfarar kasashe da jabun rigakafin.

China ta tsaurara matakan samarwa da kuma adana alluran rigakafi da kuma tsattsauran hukunci ga masu yin na jabu.

Kasar ta dauki matakin ne bayan badakalar 2016 inda aka kama wasu mutum biyu da suka sayar da miliyoyin alluran rigakafi da aka adana ba bisa ka’ida ba a kasar.

Hakan ya haifar da shakku ga kasashe game da ingancin alluran rigakafin da China ke samarwa.

Sai dai bayan bullar annobar COVID-19, kasar ta tsaurara aiwatar da dokokin da matakan domin tabbatar da ingancin rigakafin.

A halin yanzu China na kokarin samar da rigakafin COVID-19 guda bakwai, daga ciki har da wanda kamfanin sarrafa magungunan gwamnatin kasar, Sinopharm ya samu izinin amfani da shi a cikin kasar.