Rundunar ’Yan Sandan Jigawa ta kama wasu mutane tara da take zargi da satar mutane, da fashi da makami, hadi da cinikin miyagun kwayoyi a jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Emmanuel Effiom ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba a Dutse, babban birnin Jihar.
Effiom ya ce wadanda ake zargin an kamo su ne tsakanin ranar 20 ga watan Satumba, zuwa 20 ga Oktoba a sassan jihar daban-daban.
“Biyar daga ciki masu shekaru 20 ne zuwa 25, kuma an same su ne da laifin siyar da kwaya, yayin da sauran biyu masu shekaru 30 da 33 ake zarginsu da aikata fashi, da satar mota.
“Sai wasu biyar din kuma masu shekaru 22 zuwa 50, da ake zargi da satar mutane a jihar da makwabciyarta Kano,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce an kuma samu bindiga kirar AK47 a hannunsu, da bindigogi kirar gida, da tarin alburusai.
Sauran kayyakin sun hada da mota kirar Honda Civic, da babur kirar Kasea daya, da fiye da buhu 10 na miyagun kwayoyi daban-daban.
Effiom ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.
Kazalika, ya bukaci mazauna jihar da su dinga kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ga hukumomin tsaro mafi kusa da su, domin daukar matakin gaggawa.