✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama masu safarar miyagun kwayoyi 92 a Kano

An kama miyagun kwayoyi masu nauyin kilogram 987 a watan Oktoba a Kano.

Akalla mutum 92 ne Hukumar Yaki da sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kama Jihar Kano a watan Oktoba.

Kwamandan NDLEA na Kano Ibrahim Abdul, ya ce nauyin miyagun kwayoyin da aka kama a hannun mutun 92 din ya kai kilogram 987.

“Mutum tara an gurfanar da su a kotu, 101 masu kwaya kuma an kai su bangaren gyaran hali, hudu kuma an tsare su, sai kuma biyu da aka sallama”, inji Abdul.

Ya kara da cewa farautar masu fataucin miyagun kwayoyin da hukumar ke yi a jihar na haifar da kyakkyawan sakamako.