Akalla mutum 92 ne Hukumar Yaki da sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kama Jihar Kano a watan Oktoba.
Kwamandan NDLEA na Kano Ibrahim Abdul, ya ce nauyin miyagun kwayoyin da aka kama a hannun mutun 92 din ya kai kilogram 987.
- Daliban makarantar ‘yan sanda 4 sun shiga hannu bisa zargin safarar miyagun kwayoyi
- Hukumar NDLEA ta gano gonar wiwi a Kano
- ‘Yan sanda sun kama jami’an NDLEA na bogi a Kano
- An yi wa wadanda za a ba mukamai gwajin kwaya a Kano
“Mutum tara an gurfanar da su a kotu, 101 masu kwaya kuma an kai su bangaren gyaran hali, hudu kuma an tsare su, sai kuma biyu da aka sallama”, inji Abdul.
Ya kara da cewa farautar masu fataucin miyagun kwayoyin da hukumar ke yi a jihar na haifar da kyakkyawan sakamako.