✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu laifi 30,000 a 2024 – Sufeto Janar na ’Yan Sanda

Sufeto-Janar ɗin ya buƙaci jami'an rundunar su rungumi amfani da sabbin kayan aiki wajen kare al'umma.

Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa an kama mutum sama da 30,000 da ake zargi da aikata laifuka a shekarar 2024.

Daga watan Janairu zuwa Disamban shekarar nan, an kama jimillar mutum 30,313 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

Har ila yau, ya bayyana cewa an ceto mutum 1,581 daga hannun masu garkuwa da mutane, yayin da aka ƙwato bindigogi 1,984 da alburusai 23,250 a shekarar.

Egbetokun, ya bayyana haka ne, yayin wani taro da ya yi da Kwamishinonin ’Yan Sanda a Hedikwatar rundunar da ke Abuja.

Taron ya mayar da hankali ne kan nazarin nasarorin da Rundunar ’Yan Sanda ta samu a shekarar 2024 tare da tsara shirye-shiryen fuskantar ƙalubale a 2025.

Sufeto Janar, ya yabawa jajircewar da ma’aikatan ’yan sanda suka nuna, inda ya ce sun taka rawar gani wajen rage laifuka da inganta dangantaka tsakanin jama’a da rundunar.

Ya jaddada muhimmancin haɗin kai don samar za amincewa tsakanin al’umma da rundunar ’yan sanda.

“A shekarar 2024, Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta samu nasarori masu yawa wajen yaƙi da laifuka,” in ji Egbetokun.

“Mun kama mutum 30,313 da ake zargi da laifuka, mun ƙwato bindigogi 1,984, mun karɓe alburusai 23,250, sannan mun ceto mutane 1,581 daga hannun masu garkuwa.”

Dangane da shekarar 2025, Sufeto Janar ya jaddada buƙatar amfani da fasahar zamani da sababbin dabaru don hana laifuka da gudanar da bincike.

Ya buƙaci manyan jami’ai da su rungumi sabbin kayan aiki da dabaru domin inganta ayyukan rundunar.

Yayin da ake shirin shiga lokutan bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, Egbetokun ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa rundunar ta shirya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron kowa.