✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu kera bindigogi a Abiya

Jami’an da ke yaki da ’yan fashi da makami da kuma aikata sauran miyagun halaye (SARS) na rundunar ’yan sanda gundumar Obehie, Jihar Abiya sun…

Jami’an da ke yaki da ’yan fashi da makami da kuma aikata sauran miyagun halaye (SARS) na rundunar ’yan sanda gundumar Obehie, Jihar Abiya sun kama wasu mutum uku da suke kware wajen kera bindigogi kanana, suna sayarwa ga jama’a.
Mutanen dai su ne Allwell Anyanwu, Udo Nwanmuo da Ejiofor Kanu. Dubunsu ta cika ne bayan da wata majiya kwakkwara ta kyankyasa wa rundunar.
Aminiya ta samu bayanin zahirin abubuwan da ’yan sandan suka kama tare da wadanda ake zargi sun hada da bindigogi da kuma tukwanen iskar gas da gudumomi da kuma karafa manya da kanana. An ce wadanda ake zargin sun shafe sama da shekara goma suna wannan harka.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Abiya ya ce daga cikin masu laifin har ma da wanda ke masu dillanci, wani dattijo dan kimanin shekara 80 kuma ya amsa cewa hakika yana sayar wa jama’a idan sun ba shi ya sayar kuma a cewarsa, mafarauta kadai yake sayar ma wa.
Kwamishinan ya ce bindigogin na da hadarin gaske da suke kerawa suna sayarwa ga jama’a.