Sashen ’yan sanda da ke yaki da masu hakar gwal ta barauniyar hanya a Jihar Zamfara ya cafke mutum 18 masu hakar gwal ta bayan fage duk da umarnin Shugaban Kasa na haramta ayyukan hakar gwal a yankin.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Shehu Mohammed ya sanar a ranar Juma’a a garin Gusau cewa Rundunar, karkashin jagorancin SP Murtala Bello, daga Abuja mai aikin sanya ido tare da tabbatar da umarnin na Shugaban Kasa a Jihar ne ta samu nasarar.
- Boko Haram ta kai sabon hari a garin Geidan
- Matan Borno sun bukaci jami’an tsaro su sauya salon yakar ’yan ta’adda
“Kamen masu hakar gwal ta barauniyar hanyar, an gabatar da shi ne a yankin ’Yan Kaura a Karamar Hukumar Maru, inda yawancin mazauna suke hakar gwal din ta bayan fage.
“Rundunar ta yi aikinta cikin nasara tare da cafke wadanda ake zargi da karya dokar su 18.
“Da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu don su girbi sakamakon abin da suka aikata,” a cewarsa.
Ya bayyana cewa an kama mutanen da ake zargin da kayayyakin laifi da dama da suka hada da jakar sinadarai daban-daban da ake amfani da su wurin hakar gwal, sai wata mota kirar Lexus Jeep da sauran kayayyaki.