✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu garkuwa da mutane su 5 a Toro

Jami’an Kungiyar Tsaro ta Danga na Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi sun kama wadansu matasa 5 da ake zargin sun addabi al’ummar yankin da…

Jami’an Kungiyar Tsaro ta Danga na Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi sun kama wadansu matasa 5 da ake zargin sun addabi al’ummar yankin da garkuwa da mutane.

Shugaban Kungiyar Danga na yankin, Alhaji Yusuf Abdullahi ne  ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Magama Gumau.

Ya ce wadansu batagari sun damu al’ummar  yankin, don haka a kullum ’ya’yan kungiyar suna sanya ido a wurare daban-daban  a yankin, don kula da yadda mutane suke kaiwa da komowa.

Ya ce sakamakon haka ne suka gano wadannan matasa da ake zargi da garkuwa da mutane. Kuma sun  samu 3 a  Gumau,   2  kuma sun kama su ne  a wajen Zaranda.

Ya ce daya daga cikinsu ya bayyana musu cewa sun yi garkuwa da mutane sau 7. Kuma ya ce har kanin mahaifinsa sun yi garkuwa da shi, sun karbi Naira  dubu 700.

Wadanda ake zargin su ne Shagari Ibrahim da Alhassan Abdullahi da Ibrahim Sulaiman da Muhammadu Inuwa da kuma Isah Ibrahim. Ya ce tuni sun mika wa Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi matasan da ake zargin.

“Muna kira ga gwamnati ta sanya ido a kan wadanda muke kamawa, domin yawanci idan mun kama wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuffuka, ana sako su. Wannan shi ne babban damuwarmu domin idan aka kama irin wannan aka sake shi, ba tare da an hukunta shi ba, idan ya fito zai ci gaba da aikata laifi ne,” inji shi.

Sannan ya yi  kira ga iyayen kasa su kara sanya ido kuma su ba su hadin kai, don kawo karshen wannan al’amari.

Wakilinmu ya yi kokarin jin  ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan  Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti, kan wannan al’amari amma bai same shi ta waya ba.