Hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wasu mutum 14 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ayyukan fashi da makami tare da safarar miyagun kwayoyi a jihar.
Hukumar `yan sandan ta ce, ta kwato motoci biyar da wasu abubuwan da suke amfani da su daga hannun wadanda ake zargin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Ahmad Abdurrahman ya ce, wadanda aka tsare sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikata wa a hedkwatar hukumar.