✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama maniyyatan Hajji da hodar iblis a Legas

Mutum biyu da ake zargi sun haɗiye kunshi dari dari na hodar iblis din.

Jami’an Hukumar Hana da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa NDLEA sun cafke wasu maniyyata huɗu da suka yi niyyar shigar da hodar iblis kafin tashinsu ranar Laraba.

Daraktan yaɗa labarai da bayar da shawarwari na NDLEA, Femi Babafemi, ne ya bayyana yadda aka yi aka a yi kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce jami’an hukumar sun kai samame a otal ɗin Emerald da ke unguwar Ladipo a Oshodi, a jihar Legas inda wasu daga cikin mahajjatan ke zaune.

Waɗanda aka kama yayin samamen da jami’an leƙen asiri na hukumar ta NDLEA suka gudanar sun haɗa da Usman Kamorudeen mai shekara 31; da Olasunkanmi Owolabi mai shekara 46; da Fatai Yekini mai shekara 38; da wata mata Ayinla Kemi, mai shekara 34.

Wadanda NDLEA ta kama da hodar iblis
Hoto daga Channels TV

Mutanen huɗu da ake zargin an ajiye su ne a ɗakuna biyu a cikin otal ɗin sun tanadi dauri-dauri na hodar iblis din a cikin wasu kwalaye 200 da ke da nauyin kilo 2.20 domin haɗiyewa a lokacin da jami’an NDLEA suka kai samame cikin ɗakunansu.

Sai dai ya ce yayin da jami’an suka isa tuni mutum biyu daga ciki sun haɗiye dauri 100 na hodar iblis din.