✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama malamin da ya yi wa daliba ’yar shekara 7 fyade a Bauchi

Wanda ake zargin ya ja dalibar ne ofishinsa da ke makarantar Royal Science Academy.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kamo wani malamin makaranta mai shekaru 25 da ake zargi da yi wa dalibarsa mai shekaru bakwai fyade.

Kakakin rundunar, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya bayyana wa Aminiya cewa wanda ake zargin ya ja dalibar ne zuwa ofishinsa da ke makarantar Royal Science Academy a jihar, inda ya yi mata fyade.

Wakil ya ce wasu karin mutane bakwai da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar sun shiga hannu.

“Mun samu labarin cewa wani malami mai suna Sirajo Ahmad da ke koyarwa a makarantar Royal Scence ya yi wa yarinya fyade.

“Bayan shi kuma akwai wani mai  mai shekaru 35 da ke sayar da Askirim a unguwar Bacas, wanda shi ma ya yi wa wani yaro mai shekaru 12 fyade.

“Binciken da muka gudanar ya nuna mutumin ya sayi ruwan leda ne a wurin yaron, daga bisani ya ja shi wani shago ya yi masa fyade”, a cewar kakakin.

Ya ci gaba da cewa, a ranar Litinin ma ofishin rundunar da ke Tafawa Balewa a Bauchin, ya kamo wani  ikirarin sayar da magungunan gargajiya wanda ya yi wa wata mata fyade.

“Wanda ake zargin ya yi wa matar fyade ne bayan ta kai masa ’yarta mara lafiya don ya ba ta magani.

“Daga nan ne ya shaka mata maganin barci, sannan ya yi mata aika-aikar”, in ji Wakil.

Kazalika, ya ce za a gabatar da dukkanin wadanda ake zargin a gaban Kotu, domin su girbi abin da suka shuka.