✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama makasan tsohuwar babbar sakatariyar gwamnatin Oyo

An kama wadanda ake zargi da kashe tsohuwar babbar sakatariyar gwamnati Jihar Oyo Elizabeth Olaniyan Gbenle a gidanta

An kama wadanda ake zargi da yi wa tsohuwar Babbar Sakatariyar Gwamnatin Jihar Oyo, Elizabeth Olaniyan Gbenle, kisan gilla a cikin gidanta.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta gabatar da mutane su uku ne a cikin jerin wasu mutane 33 da ta kama, ciki har da wadanda ake zargi da tonon kabari suna yin tsafi da sassan jikin gawarwaki.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adebola Hamzat, ya ce shaida wa manema labarai cewa wadanda ake zargi da kisan Madam Elizabeth a cikin gidanta sun furta da bakinsu irin yadda suka kai hari gidan suka daddaure ta kafin su yi mata kisan gilla su yin awon gaba da wasu kaya a cikin motarta.

Wanda ake zargin ya jagoranci kai harin, ya shaida wa ’yan jarida cewa ya bayar da umarnin a kashe ta ne bayan ya gano cewa matar ta gane fuskarsa.

Kwamishinan ’yan sandan ya nuna wa ’yan jaridar wasu kananan motocin alfarma guda 18 da bindigogi da albarusai da wayoyin salula da tsabar kudi masu yawa da bai fadi adadinsu ba da aka samu a tare da mutanen da aka kama.

Ya ce akwai wata motar tirela kirar DAF dauke da kaya da aka kama mutanen da suka yi kokarin karkatar da ita zuwa maboyarsu kafin asirinsu ya tonu.

Kwamishinan ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da mutanen a gaban kotu ne domin yanke masu hukumci.

Sannan ya jinjina wa jama’ar gari da suke taimaka wa rundunar da bayanan sirri da yake kai ga kama bata-gari.