Dakarun rundunar tsaro ta Operation Forest Sanity sun kama wasu tarin makamai da ake kokarin yi wa ’yan bindiga safararsu a Jihar Kaduna.
An kama makaman ne a kusa da kauyen Falwaya da ke Karamar Hukumar Birnin Gwarin Jihar.
- Wanda ya lashe zaben Gwamnan Filato bai cancanci tsayawa takara ba – APC
- Shan Shisha zai iya haifar da ciwon zuciya —Bincike
A cewar Gwamnatin Jihar, jami’an tsaron sun sami nasarar ce bayan wasu bayanan sirri da suka samu kan ayyukan mutanen, inda daga bisani kuma suka kama wata mota da ba a yarda da ita ba a hanyar, inda aka tarar da makaman a cikinta.
Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya fada a cikin wata sanarwa ranar Alhamis cewa an kama motar ce kirar Toyota Corolla dauke da harsasai sama da 200 da aka boye a sassanta daban-daban.
Ya ce bayan zuzzurfan bincike, an gano harsasai 1,079 da wasu guda 886 da guda 139 masu girma daban-daban.
Samuel ya kuma ce an kama wasu bindigu kirar AK-47 guda biyar a hannun wanda ake zargin.
Kwamishinan ya ce yanzu haka direban motar, wani mai suna Aminu Abdullahi na hannun jami’an tsaro yayin da ake ci gaba da bincike.
Ya ce tuni Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufa’i ya karbi labarin da hannu biyu, sannan ya jinjina wa jami’an tsaron kan namijin kokarin da suka yi wajen samun nasarar.