✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama mai unguwa dauke da tabar wiwi

Jami'an Hukumar NDLEA sun kama mai unguwar dauke da tabar wiwi

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta ka,a wani mai yi wa kasa hidima (NYSC) da tabar wiwi a Jihar Kano.

Wannan dan NYSC an kama shi ne da tabar wiwi mai nauyin kilogram daya a rukunin gidajen masu yi wa kasa hidima da ke Karamar Hukumar Sama’ila.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya kuma sanar da kama wani mai unguwa dauke danyar tabar wiwi mai nauyin kilogram biyar.

Femi Babafemi ya ce, mai unguwar yankin Akarabata da ke Karamar Hukumar Ile-Ife a Jihar Osun Cif  Ige Babatunde, mai shekaru 50, ya shiga hannun NDLEA ne a ranar Juma’a.

Ya kara da cewa jami’an hukumar sun kuma kama wani dan kasar Chadi dauke da sinki 20 na cirarrun tabar wiwi (Loud) da ya dauko daga Jihar Kano.

Dan kasar Chadin, a cewarsa ya fada hannun hukumar ne a wani shingen bincike a hanyar Ngurore zuwa Yola a Jihar Adamawa.

A Jihar Legas kuma an kama gungun masu safarar hodar iblis da wasu ma’aurata ke jagoranta inda aka kwace miyagun kwayoyin da suke shirin yin safarar su a cikin gida da kasashen waje.

Babafemi ya kara da cewa ma’auratan da wasu abokan cin mushensu suna hannun hukumar su ma.

A Jihar Ondo kuma an kama wasu mutum biyu a samamen da hukumar ta kai Dajin Ikota a Karamar Hukumar Ifedore inda aka lalata tabar wiwi mai nauyin 42,500kg a wata gona mai girman hekta 17.

A ranar Asabar kuma a Abuja an kama wasu mutane biyu a hanyar Abaji-Gwagwalada da da kwalabe 1,132 na kwayar kofin ta ruwa; kwayar Tramadol 13,540; Diazepam kwaya 50,000 da kuma  Rohypnol 59.

A karshe ya ce an kama wa wani matashi dauke da hodar iblis mai nauyin gram 350 a wani shingen bincike a garin Otukpo da ke Jihar Binuwai