Rundunar ’Yan Sandan jihar Bauchi ta kama wani mutum mai shekara 59 bisa zarginsa da laifin yi wa wata yarinya mai shekara daya da rabi fyade.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, Sufeto Ahmed Mohammed Wakil ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Bauchi ranar Lahadi.
- An kama dan daudun da yake zagin kabarin mahaifiyar abokin fadansa na TikTok
- Katsina: An sace matar tsohon shugaban PDP a Batsari
Wakil ya ce mahaifiyar mamacin Nenkat Danladi, mai shekara 31, ta kai rahoto ga ofishin ’yan sanda na Yelwa a ranar tara ga watan Agustan 2022 da misalin karfe 7:00 na dare.
Mahaifiyar ta yi korafin cewa a ranar shida ga watan Agustab 2022 da misalin karfe 11:30 na safe, ta hadu da makwabcinta, Alhamdu Yusuf, mai shekaru 59 a gado tare da diyarta Blessing (ba sunanta na gaske ba) mai shekaru daya da rabi.
Kakakin ’yan sandan ya ce, “Bayan kamar minti 30, sai ta gano cewa gaban ’yarta yana zubar da jini.
“Bayan ta shigar da korafin, wata tawagar jami’an ’yan sanda karkashin jagorancin DPO na Yelwa suka garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi domin duba lafiyarta.
“An kama wanda ake zargin kuma an fara bincike da gaske a kan lamarin,” inji sanarwar ’yan sandan.