Jami’an ’yan sanda a Jihar Ogun sun kama wani mutum bisa zargin yi wa wata tsohuwa mai shekara 60 fyade.
Wanda ake zargin mai shekara 40, ya shiga hannu ne bayan dan tsohuwar ya shigar da kara a caji ofis na Idanyin da ke Karamar Hukumar Ado Odo-Ota a Jihar.
- A bai wa ’yan IPOB damar ballewa daga Najeriya — Nastura Ashir
- Yawancin ’yan bindigar da ke addabar mu ba ’yan Najeriya ba ne – Gwamnan Neja
Dan dattijuwa ya shaida wa ’yan sanda cewa tana cikin dakinta ne lokacin da mutumin ya kutsa ya yi mata fyade da karfin tsiya.
Kakakin ’yan sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa manema labarai a Abeokuta cewa bayan samun rahoton ne Babban Jami’in ’Yan Sandan yankin, Olayinka Kuye, ya baza jami’ansa domin farautar mutumin.
Ya ce daga bisani an gano shi sannan ’yan sandan suka tasa kyayarsa.
Mutumin ya amince da aikata laifin, ita kuwa dattijuwar an garzaya da ita asibiti domin duba lafiyarta.
Kakakin ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Edward Ajogun, ya bayar da umarnin a mayar da wanda ake zargin Sashen Kula da Miyagun Laifuka na Rundunar domin ci gaba da bincike da kai shi gaban kuliya.