An kama wani jami’in sa ido a jarabawar kammala sakandare a lokacin da yake tsaka da tafka magudi a Jihar Kano.
Hukumar shirya Jarabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) ta kama jami’in, wanda ta ki bayyana sunansa ne a yayin da ya hada baki da wasu abokan aikinsa suka tura tambayoyin darasin harshen Ingilshi a wasu zaurukan Whatsapp.
“Ba za mu bayyana wanda ake zargin bas ai an kammala bincike, amma ina tabbatar muku da cewa an kama shi ne a kwaryar garin Kano”, inji Babban Jami’in WAEC mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Abayomi Lateef Zubairu
Sai dai ya ce ko kafin hukumar ta cika hannu da mutumin, ya riga ya taru tambayoyin jarabawar taWhatsapp.
Zubairu ya gargadi masu sa ido a jarabawar da su guji mummunar dabi’ar domin akwai hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama.
Ya ce bayan hukumar ta gama bincikenta a kan wanda ake zargin za ta yanke shawara kan damka shi a hannun ’yan sanda.