✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘An kama mai garkuwa da ‘yan matan Katsina’

’Yan sanda sun kama wani matashi bisa zargin sa da hannu a garkuwa da wasu ’yan mata biyu a Karamar Hukumar Kurfi ta Jihar Katsina.…

’Yan sanda sun kama wani matashi bisa zargin sa da hannu a garkuwa da wasu ’yan mata biyu a Karamar Hukumar Kurfi ta Jihar Katsina.

Kakakin ’yan sandan jihar, Gambo Isah ya ce matashin tsohon mai garkuwa da mutane ne da aka sako daga cikin fursunonin da gwamnati ta yi wa afuwa.

“Ya taba aika wa mahaifiyar ’yan matan sakon waya yana barazanar ta ba shi kudi ko kuma a yi garkuwa da su. Kuma ’yan sanda sun kwace wayar da kuma sakon da ya aika matasyin hujja”, inji shi.

A daren Lahadi ne ’yan bindiga suka kai farmaki a Sabuwar Unguwa Sabon Layi a garin na Kurfi da misalin 2.00 na dare, inda suka yi awon gaba da ’yan mata biyu daga gidan iyayensu.

Jihar Katsina na yawan fama da matsalar ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a yannkunan jihar inda suke garkuwa da mutane suna kuma karkashe wasu.