✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mahaifiyar da ke wa ‘yarta kawalci a Kurosriba

’Yan sanda a Jihar Kurosriba sun cafke wata mata mai suna Udoaka Sunday tare da wasu mutum uku da ake zargi da cin zarafin diyarta…

’Yan sanda a Jihar Kurosriba sun cafke wata mata mai suna Udoaka Sunday tare da wasu mutum uku da ake zargi da cin zarafin diyarta ’yar shekara 12 da haihuwa.

Matar dai ana zarginta ne cewa tana gayyato maza suna yin lalata da ’yar tata, tana karbar kudi daga wurinsu. Kamar yadda Aminiya ta binciko, matar takan takan amshi Naira dubu 15 ko abin da ya fi haka daga hannun duk wani namiji da zai yi lalata da diyarta.

Wani makwabcin wacce ake zargin, ya bayyana wa Aminiya a sirrance cewa: “Ba ta dade da karbo Naira dubu 15 ba a wurin wani tsohon soja mai suna Effiom Okon, da ma wasu mutum hudu, duk a zatonta ba a san abin da take yi ba. Tana bin samari da masu abin hannu tana karbar kudi daga hannunsu, tana hada su da ’yarta suna lalata da ita.”

Majiyar labarinmu ta ci gaba da cewa haka Udoaka take bin mutane, musamman wadanda suke karbar kudin fansho, tana karbe masu kudi, tana tura ’yar wurinsu kuma ba tun yanzu take yin haka ba. An bayana cewa ta dade tana yin wannan harka, amma takan gargadi ’yar tata da cewa kada ta rika fashin zuwa wurin mutanen tana biya musu bukatarsu.

Da wakilinmu ya tambayi mahaifiyar yarinyar yadda aka yi har aka tona asirinta, sai ta ce: “Yarinyar ce da ta ga abin ya ishe ta sai ta gaya wa malaminsu na makarantar boko, shi kuma malamin ya sanar wa kungiyar kare cin zarafin yara kanana. Daga nan kuma suka sanar wa ’yan sanda. Haka kawai ina zaune gida suka zo suka tafi da ni.”

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ’yan sandan Kurosriba, Irene Ugbo ta tabbatar mana da labarin, inda kuma ta ce tsohon soja Effiom Okon da uwar yarinyar Udoaka Sunday, suna nan hannunsu ana tsare da su domin ci gaba da bincike.