‘Yan sanda sun kama wata mata mai matsakaicin shekaru da ’yarta kan zargin dukan wata malamar makaranta har suka kashe ta a jihar Anambara.
Marigayiyar mai suna Rita, wacce ke koyar da harshen Igbo a makarantar sakandire mai suna Starlight da ke kauyen Ogidi da ke garin Idemili ta Arewa da ke cikin jihar ta yanke jiki ta fadi bayan da matar da ’yarta da wani mutum suka rika dukanta da tsintsiya.