Wani ma’aikacin lafiya ya rasa aikin sa bayan da ya amsa laifin cire kayan sa na kariya daga cutar COVID-19 domin ya yi luwadi da wani mai dakue da cutar a bandaki.
Lamarin dai ya faru ne a wani asibiti mai suna Wisma Atlet na birnin Jakarta na kasar Indonesia.
- Masar ta kulle masallaci saboda karya dokokin kariyar COVID-19
- Bayahude mai shekaru 75 ya mutu sa’o’i biyu da yi masa riga-kafin COVID-19
“Da gaske ne an sami zargin yin luwadi tsakanin wani ma’aikacin lafiya da wani mai dauke da cutar COVID-19 a asibitin Wisma Atlet,” inji shugaban Kungiyar Ma’aikatan Jinya ta Kasar, Asep Gunawan.
Ya ce an dauki matakin korar sa daga aikin ne saboda laifin da ya aikata ya saba da ka’idojin aikin kungiyar su a kasar.
Dubun ma’aikacin jinyar ta cika ne lokacin da wanda ya yi luwadin da shi ya wallafa abinda ya wakana tsakanin su a shafin sa na Twitter a ranar Juma’a, kamar yadda jaridar Sun ta Burtaniya ta rawaito.
A cikin sakon dai, mutumin ya kuma dora tattaunawar da suka yi ta WhatsApp, wanda a ciki ya nuna hoton kayan kariyar ma’aikacin yashe a kasa lokacin da suke lalatar.
Kwamandan Rundunar Sojojin kasar na yankin Jakarta, Laftanar Kanal Arh Herwin ya ce, “Tuni muka mika wannan batun zuwa ’yan sandan birnin Jakarta. Mun sami ma’aikacin lafiyar ya bamu bayani sannan muka ci gaba da yi masa tambayoyi.
“Shi kuwa a nasa bangaren, mara lafiyar yanzu haka yana can ana ci gaba da killace shi a wani gidan tsohon dan kwallo da yanzu aka mayar da shi wurin killace masu dauke da cutar,” inji shi.
Daga bisani dai duka su biyun an yi musu gwajin cutar inda aka gano har yanzu mara lafiyan yana dauke da ita, yayin da shi kuma ma’aikacin jinyar binciken ya nuna bai kamu da ita ba.
Idan dai har aka same shi da laifi a gaban kuliya, ma’aikacin na iya fuskantar hukuncin daurin da ya kai shekaru 10 a gidan yari.