Jami’an Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Kasa, sun samu nasarar cafke wani abokin aikinsu da aka kulla kitimurmurar shigar wa da fursunoni fiye da giram dubu 4.8 na tabar wiwi da kuma wayoyin salula na zamani har guda takwas.
Kakakin Hukumar reshen jihar Kano, Musbahu Lawal Kofar Nassarawa ne ya tabbatar wa da Aminiya hakan ba tare da fayyace sunan ma’aikacin da aka kama ba.
Sai dai ya ce an gano ma’aikacin na da hannu wajen yi wa fursunoni safarar kayan maye a gidan yarin Kurmawa da ke kwaryar birnin Dabo.
“Mun kama wani ma’aikacinmu daya da ke da hannun wajen kai wa wasu fursunonin da aka yankewa hukuncin kisa tabar wiwi wadda nauyinta ya kai giram dubu 4.8 da wayoyin salula takwas, lamarin da ya haifar da tarzoma a gidan yarin.
“Shekaru biyu da suka gabata ne ma’aikacin ya fara aiki, kuma tuni mun mika shi a hannun Hukumar Hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA domin daukar matakin da ya dace a kansa.
“Za’a gurfanar da shi a gaban kotu, kuma idan an tabbatar da laifinsa da ake zarginsa ana iya dakatar da shi daga aiki.
“Za mu ci gaba da bincike domin gano tsawon lokacin da hakan ta kasancewa tana faruwa sannan kuma mu gano dukkanin wadanda ke da hannu a lamarin,” in ji Kofar Nassarawa.
Ana iya tuna cewa da yammacin Alhamis da ta gabata ce fursunoni suka ta da tarzoma a gidan yarin kan shigo da wasu miyagun kwayoyi.
Aminiya ta ruwaito cewa tarzomar ta barke ne a gidan jim kadan da yin bude baki, inda fursunoni suka ta da kayar baya kan kwace wata tabar wiwin da aka shigo musu da ita.
Musbahu Lawal ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni suka kafa kwamiti don gano yadda tabar wiwin ta shiga gidan.
A cewarsa, “Wani ne ya shigo da tabar wiwi ga fursunoni amma jami’anmu suka kwaceta, shine suka ta da tarzoma a kan lallai sai an basu.
“Tuni mun kafa kwamiti domin gano yadda aka yi tabar ta shigo gidan; ko a cikin irin abincin bude bakin da ake kawo wa fursunoni ne aka sako ko kuma da jami’anmu aka hada baki.
“Tarzomar ba ta da alaka da kowanne irin yunkuri na balle gidan yarin ko na guduwa,” inji shi.
Daga bisani wasu sun yi zargin cewa fursunonin sun yi yunkurin balle gidan ne domin guduwa da nufin nuna bacin ransu kan irin abincin da ake ba su da azumi, duk kuwa da irin tarin gudunmawar da suka karba daga masu hannu da shuni.
Sai dai kakakin ya musanta wannan zargin inda ya ce ba shi da tushe ballantana makama.
Gidan yarin Kurmawa dai wanda ya haura shekara 100 da ginawa shine babban gidan yari a jihar Kano kuma yana bayan Fadar Sarkin Kano.