Hukumar Yaki da Rashawa (ICPC) ta tsare wani mai mukamin Mataimakin Kwamanda a Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDSC) kan zargin damfarar masu neman mallakar gidaje a Abuja miliyoyin kudade.
Dubun Mataimakin Kwamandan mai suna Edike Mboutidem Akpan ta cika ne bayan ya yaudari wasu masu sayen filaye ya amshe musu Naira miliyan 26.7 ta hanyar amfani da kamfaninsa, Danemy Nigeria Limited.
- Harin sojoji ta sama ya kashe ’yan ta’adda 82 a Zamfara
- ’Yan bindiga sun kashe sojoji 7 a Taraba
- NAJERIYA A YAU: Ayyuka Na Musamman A Kwanaki 10 na Farkon Watan Dhul-Hijja
“Mataimakin Kwamanda Akpan ya yi amfani da kamfaninsa, Danemy Nigeria Limited, ya karbi Naira miliyan 11.350 daga Mista Igwe Onus Nwankwo, a matsayin kudin filaye 10 a kan Titin Airport Road.
”A lokuta daban-daban kuma ya karbi N1,305,000 daga Dokta Robert Okoro da N1,303,000 daga Dokta Akuneme Marcel Ikwuoma, a matsayin kudin filaye karkashin tsarin Rukunin Gidaje na Family Defenders a Airport Road.
”Ana kuma tuhumar shi da karbar N2,610,000 daga Misis Chidinma Obasi a matsayin kudin filaye biyu, da wani N1,205,000 daga Mista Etuechere Martins, a kan fuloti guda,” kamar yadda takardar gurfanar da shi a kotu ta bayyana.
Kakakin ICPC, Azuka Ogugua, ya ce Akpan ya rika fakewa da wani hadin gwiwa na bogi tsakanin kamfaninsa da Hukumar NSCDC yana yaudarar masu son sayen filayen yana yi musu alkawarin filaye a yankunan Sabon Lugbe da da Airport Road a Abuja da kuma yankin Karshi na Jihar Nasarawa.
A yayin gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a V.S Gaba na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ICPC ta tuhumi Mataimakin Kwamanda Akpan da aikata laifuka 17, amma ya musanta duk laifuffukan.
Daga nan sai lauyansa ya bukaci kotu ta ba da belin shi kuma lauyan ICPC, John-Paul Okwor, bai ja ba.
A karshe Mai Shari’a Gaba ya ba da belin Mista Akpan a kan Naira miliyan biyar tare da mutum biyu da za su tsaya kishi, kuma dole daya daga cikinsu ya kawo takardar shaidar mallakar gidan da yake zaune a ciki.
Shi kuma wanda ake zargin zai mika wa kotun takardar fasfo dinsa.
Kotun ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Nuwamba, 2022.