Rundunar ’yan sanda a Jihar Edo ta sanar da cafke wani korarren kofur mai suna Omokaro Edison bisa zarginsa da karbar kudi a hannun mutane.
Da yake jawabi ga manema labarai, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Edo, Kotongs Bello ya ce wanda ake zargin an kama shi ne a ranar 22 ga watan Afrilun da muke ciki.
- ISWAP ta dauki alhakin kashe ’yan sanda a Kogi
- Matsalar Tsaro: Birtaniya ta horas da dakaru 145 a Najeriya
Kuma a cewarsa, wanda ake zargin yana yi wa jama’a karyar shi dan sanda ne bayan tuni an kore shi daga bakin aiki.
Kazalika ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da yake karbar kudi a hannun mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, kuma take ya amsa laifinsa bayan shigarsa hannu.
Kotongs Bello ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, Abutu Yaro ya ce rundunar za ta ci gaba da aiki tukuru da gudanar da sintiri domin zakulo bata garin da ke bata wa rundunar suna.