Rundunar ’yan sandan Nijeriya reshen Abuja ta sanar da kama wani da ake zargin kasurgumin mai garkuwa da mutane ne a babban birnin kasar mai suna Chinaza Phillip.
Aminiya ta ruwaito cewa, rundunar ’yan sandan Kaduna ce ta cafke Chinaza a kan hanyarsa ta zuwa Kano tare da wasu abokan harkallarsa a ranar Alhamis.
- ’Yan bindiga sun sace mutum uku a Abuja
- Dalilin da za mu waiwayi batun raba Masarautar Kano — Kwankwaso
Bayanai sun ce an yi musayar wuta tsakanin mutanen tawagar Phillip da ’yan sanda, lamarin da ya kai ga ceto Segun Akinyemi, wani mazaunin Abuja, wanda a Larabar da ta gabata aka yi garkuwa da shi yayin da yake tuƙi a hanyarsa ta komawa gida
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan ya fitar, ta ambato yadda ’yan sandan suka tari hanzarin mutanen Chinaza a kan hanya
Kazalika, a sanarwar da rundunar ’yan sandan Nijeriya ta wallafa a shafinta na X, ta ce rundunar ’yan sanda ta Jihar Kaduna ce ta yi nasarar kama mai satar mutanen ranar Alhamis 18 ga watan Janairun 2024.
“Daga nan sai rundunar ta Kaduna ta miƙa shi ga rundunar ƴan sanda ta Abuja a yau Juma’a 19 ga watan Janairun 2024, kuma a yanzu haka yana hannun ƴan sanda,” in ji sanarwar.
Rundunar ’yan sandan ta ce za ta yi ƙarin bayani a nan gaba kaɗan, sai dai ta wallafa hoton Chinaza da kuma na wasu bindigogi da ba ta yi bayani a kansu ba.
Wannan babban kamu yana zuwa ne a lokacin da ake ta samun ƙorafe-ƙorafe da koke-koke a kan yawan satar mutane don karɓar kudin fansa da ake yi a Abujan, ciki har da na wasu ’yan mata shida ’yan gida ɗaya da ya ɗaga hankalin al’ummar ƙasar.