✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama hanyar samar da maslaha tsakanin Fulani makiyaya da manoma a Edo.

A makon da ya gabata Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adamu Aliyu Oshiomhole ya gana da shugabannin al’ummar Fulani makiyaya da na kungiyar manoma da na…

A makon da ya gabata Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adamu Aliyu Oshiomhole ya gana da shugabannin al’ummar Fulani makiyaya da na kungiyar manoma da na kanana hukumomin 18 na jihar baki daya, a kan batun korafe-korafen da ya shafi tsakanin manoma da makiyaya a jihar.
A wannan zaman ganawar, gwamnan ya nuna matukar damuwarsa game da yadda ya ce ya samu rahoto a kan matsalar da ke faruwa tsakanin Fulani da manoma, don haka ya shawarci bangarorin dukansu biyu da su kai zuciya nesa, su goyi bayan shirin zaman lafiya. Ya ce: “A wannan jihar ba mu da wani nuna bambanci, don haka kowane dan Najeriya yana da ’yancin zama a wannan jihar. Don haka abin da muke bukatar mu gani shi ne, da farko zaman lafiya da hadin kai da kaunar juna.”
Gwamnan ya umarci shugabannin kananan hukumomi 18 na jihar da su kafa kwamitin lura da sha’anin makiyaya da manoma a hedikwatocin wadannan kananan hukumomin, domin su kawo wa kwamiti da za a kafa na hedikwatar jihar rahoton abin da suka gani yake tasowa da sauran hakan domin a samu bakin zaren warware matsalar tsakanin Fulani makiyaya da manoma a Jihar Edo.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Alhaji Badamasi Saleh shugaban al’ummar Arewa mazauna Edo, bayan gode wa gwamnan da ya yi sai ya ce: “A shirye muke mu shagabannin al’umma mu ci gaba da wayar wa al’ummarmu kansu a kan muhimmancin zaman lafiya da goya wa gwamnati baya kuma za mu kira taro, musamman na zama da masu shanu ’yan kasuwa da ainihin shugabannin Fulani makiyayan, mu ba su shawarwari mu fadakar da su a kan abin da ya kamata su yi da kuma tsare dabbobinsu, su daina yi wa manoma barna kamar yadda ake zargin suna aikatawa.” Inji shi.