Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta ce ta kama wani fasto na Majami’ar House on Rock da ke Abuja wanda ya hau kan dandamalin Coci dauke da bindiga kirar AK47.
Fasto din mai suna Uche Aigbe ya ruda baki dayan Cocin a lokacin da mabiyansa suka gan shi dauke da bindigar.
- Mutanen da girgizar kasa ta kashe a Turkiya da Syria sun zarta dubu 36
- Matasa sun yi garkuwa da soja a Anambra
Lamarin ya auku ne a zagaye na biyu na ibadar da suke yi a Majami’ar da kuma a bisa al’ada ya fi yawan mutane da kan fito daga sassa daban-daban na Abuja.
Rudu da mutanen Cocin suka shiga a lokacin da suka ga faston dauke da bindiga, ya sa harabar Cocin zama kamar fagen wasar kwaikwayo.
Fasto Uche Aigbe dauke da bindigar ya kama wasu sabbatu cewa “ wasu mutane na son fada da ni, to gani na zo.
“A yau akwai wasu jagororin Coci-coci da ke dauke hankalin mabiyanmu, wannan ne ya sa mu ka dauko bindiga don kariyar kanmu. Zan kuma yi wo shiri na musamman akan wasunku masu kwana a Coci”
To sai dai Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda ta babban birnin tarayya na Abuja Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewar, daukar bindiga AK-47 haramun ne a Kundin Tsarin Mulkin Najeriya kuma ko jami’an tsaro ma, ba kowa aka sakar wa mara a kan daukarta ba.
Yanzu haka dai rundunar ‘yan sanda ta Babban Birnin Tarayya, Abuja na kan bincike kan lamarin da kuma sanin matakin da za a dauka a kan fasto.