✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

An kama fasto kan yi wa karamar yarinya cikin shege

Dattijon mai shekara 61 ya ce zai kula da mai cikin da abin da za ta haifa.

’Yan sanda a Jihar Ondo sun cafke wani fasto bisa zargin shi da laifin yi wa wata budurwa mai shekara 16 fyade har ta dauki cikin shege.

Jami’an na zargin faston mai shekara 61 ya yi wa budurwar fyaden ne a lokacin da aka kai ta cocinsa domin ya yi mata addu’a.

Ana tuhumar shi da yi mata fyade a gidansa, tare da kai ta kasuwa a cikin dare inda ya sake amfani da ita.

Da farko limamin cocin ya amsa laifin a gaban ’yan sanda, amma daga baya ya musanta zargin, inda ya ce addu’a kawai ya yi mata bayan “Na lura cewa tana da bukatar addu’a.”

Ya ci gaba da cewa, “Duk lokacin da za mu fara addu’ar takan turje ta nuna rashin yarda amma ni ban taba kwanciya da ita ba.

“Na amsa laifin ne a wurin ’yan sanda saboda azabar da suka yi min, amma duk da haka a shirye nake na kula da abin da za a haifa,” a cewarsa.

Ya shaida wa manema labarai cewa zai kula da mai cikin har zuwa lokacin da za ta haihu, daga baya sai a je a yi gwajin kwayar halittar yaron domin a tabbatar da mahaifinsa, daga nan a yanke hukunci.