✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama dattijo da mutum 10 bisa zargin lalata ’yar shekara 11

’Yan sanda a jihar jigawa sun damke wasu mutane su 11 da ake zargi da laifin yin lalata da wata karamar yarinya ’yar shekara 11…

’Yan sanda a jihar jigawa sun damke wasu mutane su 11 da ake zargi da laifin yin lalata da wata karamar yarinya ’yar shekara 11 a duniya.

Kame mutanen 11 dai ya biyo bayan kama wani mutun ne mazaunin kauyen ma ai da ke yankin karamar hukumar Dutse a lokacin da yake kokarin yin lalata da yarinyar a karo na biyu bayan da ’yan sanda suka dana mar tarko ya fada ciki

’Yan sanda sun kame mutumin ne mai shekara 57 a lokacin da yake kokarin lallabar yarinyar a Limawa lokacin da ta je cin kasuwar kauyen.

Da yarinyar ta ki sai ya yi yunkurin afka mata da karfin tsiya, amma a daidai lokacin ’yan sanda suka yi dirar mikiya suka damke shi.

Bayan da ’yan sandan suka matsa da bincike, ita yarinyar ta nuna sauran mutane 10 wadanda dukkansu suka yi lalata da ita bayan dattijon da ake kira Zuwai.

Tuni dai dukkansu 11 suka bayyana a gaban yansanda kuma duk sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa

Kakakin rundunar ’yan sanda na jahar Jigawa SP Abdu Jinjiri ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

“Yanzu haka wadannan mutane 11 suna hannunmu ana ci gaba da bincike ana tatsar bayanai a wajen su, kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu domin a yi masu hukuncin da ya dace da su”, inji SP Jinjiri.