Hukumar NDLEA mai hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, ta sanar da cafke wani mutum mai shekara 70 da ake zargi da yi wa ‘yan bindiga safarar miyagun kwayoyin.
Sanarwar da NDLEA ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta kama mutumin mai suna Muhammad Rabi’u Wada da ake zargi yana kai wa mayakan Boko Haram da ‘yan bindiga a Jihar Neja.
- Gobara ta tashi a kusa da Masallacin Annabi na Madina
- Gasar AlKur’ani: Ganduje ya ba gwaraza kyautar Naira miliyan 5
Hukumar ta ce mutumin na shigo da miyagun kwayoyi Najeriya daga Jihar Agadez ta Jamhuriyyar Nijar.
Haka kuma, hukumar ta sanar da lalata wata gonar tabar wiwi mai girman hekta 95 a Jihar Ondo da ke Kudancin kasar.
An gano gonar ce a dajin Ogbese, sai dai babu wanda aka samu nasarar kamawa inda bincike yake ci gaba da gudana don gano mai gonar.
Kazalika, Hukumar ta samu nasarar kwato tabar wiwi da ta kai nauyin kilo dubu 116.1 a wani shingen ababen hawa a kan hanyar Okene zuwa Lokaja da ke Jihar Kogi.
Mutumin wanda ya shiga hannu a hanyarsa ta zuwa Kaduna mai suna Sulaiman Sa’id, ya ce ya dauko kayan ne daga jihar Edo.