✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan hidimar kasa na jabu a Akwa Ibom

Jami’an ’yan sanda a Jihar Akwa Ibom sun kama mai yi wa kasa hidima na bogi mai suna Justice Orlu, a sansanin masu yi wa…

Jami’an ’yan sanda a Jihar Akwa Ibom sun kama mai yi wa kasa hidima na bogi mai suna Justice Orlu, a sansanin masu yi wa kasa hidima da ke garin Ikot-Itie- Udung, karamar Hukumar Nsit Atai.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, DSP Chukwu Ikechukwu ya sanar da haka ga Aminiya. Ya ce matashin ya shiga hannu ne sakamakon wasu bayanan sirri da rundunar ta samu na jabun mai yi wa kasar hidima. Ya ce: “Justice Orlu Ordu, dan asalin Jihar Ribas, yankin Ikwere ne, kuma a daya daga cikin dakunan masu yi wa kasar hidima ne aka kamo shi.”

Jami’in ’yan sandan ya ci gaba da cewa wanda ake zargin bakinsa ya yi bayani ba wani ne ya tilasta masa ba. Ya ce ya buga jabun takardar yi wa kasa hidima da ta nuna shi dalibi ne daga Jami’ar, Uyo Tsangayar Ilmin Zayyane-Zayyane.

Ya ce a yanzu haka suna kan bincike kuma da zarar sun kammala, za su mika shi ga kotu, domin ci gaba da nata bangaren aikin.