✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan Ghana da ya ce an ba shi yara uku a kan Naira dubu 26

An kama wani dan kasar Ghana da ake zarginsa da mallakar yara uku ta hanyar sayensu a kan Naira dubu 26. Wadansu da Aminiya ta…

An kama wani dan kasar Ghana da ake zarginsa da mallakar yara uku ta hanyar sayensu a kan Naira dubu 26.

Wadansu da Aminiya ta tuntuba da suka nemi a sakaya sunansu game da lamarin sun shaida mata cewa a ranar 15 ga August bana ne, wanda ake zargin mai suna Mista Douglas Attah Opore mai shekara 56 dan asalin kasar Ghana da ya ce shi dan kasuwa ne, da yake zaune a Layin Turunku daura da Pack Road, PZ, Zariya a Jihar Kaduna, ya je ofishin kula da jin dadin jama’a da walwala domin neman a yi masa takardar izinin mallakar yaran uku maza biyu da mace daya. 

Babban yaron mai suna Samuel Attah shekararsa hudu, sai ta biyu mai suna Ketura Attah mai shekara uku, sai na uku mai suna Adeson Attah mai shekara biyu, inda daga nan ne asirinsa ya fara tonuwa.

Majiyarmu ta ce ganin ba a yarda da irin bayanin da ya yi ba ne, sai aka sanar da ’yan sanda wadanda suka kama wanda ake zargi domin bincike.

A ofishin ’yan sanda na Tudun Wada an shaida wa Aminiya cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ce, wani ma’aikacin ofishin walwala da jin dadin jama’a mai suna Sarki Mohammed Awai ya sanar da su cewa ga wani wanda ba a amince da shi ba ya zo ofishinsu tare da yara uku yana so a ba shi takardar izinin mallakarsu, ganin bai amince da irin bayanin da ya yi ba ne, ya nemi ’yan sanda su shiga maganar su bincika kuma yanzu haka suna bincikawa.

Aminiya ta ji na bakin, inda ya ce ya samu yaran ne ta hanyar wani ma’aikacin gidan kula da marayu da ke kofar Kibo, Zariya, kuma ya ce ya fara kawo masa yaro na farko ne bayan an haife shi da kwana biyu wato ranar 1 ga Augustan shekarar 2013, “Yanzu shekararsa hudu a hannuna, kuma na ba shi Naira dubu 10 , kuma nasa wa yaron suna Samuel, sannan bayan wani lokaci ya kara kawo yarinyar ita ma bayan haihuwarta da kwana biyu, wato a ranar 8  ga Janairun shekarar 2014, wacce yanzu shekarunta uku a hannuna ita ma na ba shi Naira dubu shida, sai na sa mata suna Ketura. Sai kuma na uku ya kawo min namiji wanda ba zan iya tuna ranar ba, amma a shekarar 2015 ne, kuma na ba shi Naira dubu 10, kuma na sa wa yaron suna Adeson.”

Mista Douglas ya ce abin da ya sa shi neman yara shi ne ya auri matarsa mai suna Misis Gladys Attah mai shekara 46, kuma ’yar kabilar Ibo ce  daga karamar Hukumar Edimili a Jihar Anambra, amma shekararsu 26 ba su samu haihuwa ba, don haka suka yanke shawarar neman yara amma ba wai sun dauke su da wata muguwar manufa ba ce.

A gidan marayu na kofar Kibo da ke Zariya da Mista Douglas ya ce wani da ke aiki a gidan ne ya ba shi su, da wakilinmu ya nemi jin ko an bi ka’ida wajen mika masa yaran, sai shugabar ma’aikatan ta ce ba za ta ce komai kan wannan matsala domin maganar ta kai hedikwatarsu a Kaduna.

Babban Jami’in ’Yan sandan Tudun Wada ya ce bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ba ya da wata takarda da ta nuna cewa ya samu amincewar daukar yaran ko ga  wanda ya ba shi yaran. Don haka sun gama binciken sun tura hedkwatarsu a Kaduna domin cigaba da bincike.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Runduanr ’Yan sandan Jihar Kaduna kan lamarin, ASP Y. A. Sabo, ya ce an yi masa sauyin wurin aiki amma zai bincika tunda wanda ya canje shi bai fara aiki ba. Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba wani bayani daga gare shi.

Aminiya ta buga waya sau biyar ga Kwamishinan Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba tare da tura mata sako kan lamarin amma ba ta mayar da jawabi ba.