✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dafa-duka da aka shigo da ita daga Indiya

Wasu ‘yan sumoga sun yi fasa kwaurin hadadden kayan. abincin, wadanda suka hada da shinkafa dafa-duka da sakwarar doya da miyar agushi da miyar ogbono…

Wasu ‘yan sumoga sun yi fasa kwaurin hadadden kayan. abincin, wadanda suka hada da shinkafa dafa-duka da sakwarar doya da miyar agushi da miyar ogbono da suka yi odar su daga kasar Indiya, domin sayarwa ga mabukata a Najeriya. Sai dai sun yi rashin nasara a lokacin da Rundunar Kwastam ta Tin-Can da ke gabar teku a Legas, ta kama wadannan kaya da aka cunkusa su cikin kontena guda 20 aka shigo da su cikin kasa ba tare da izni ba.

Bayanin haka yana kunshe ne cikin wata takardar sanarwa da aka raba wa ‘yan jarida a Legas, wacce Kakakin rundunar kwastam ta Tin-Can Mista Uche Ejesieme ya sanya wa hannu. Sanarwar ta ce, Kwamandan Rundunar Tin-Can, Kwanturola Bashar Yusuf, ya ce, wadanda suka aikata wannan aiki na shigo da kayan abincin da aka sarrafa daga wata kasa, sun aikata mummunan aiki, musamman saboda gwamnatin tarayya ta amince da yin odar na’urorin sarrafa amfanin gona zuwa kayan abinci daga kasashen waje ba tare da biyan harajin ko kwabo ba. Ya nuna mamakin ganin an yi odar kayan abincin gida zuwa cikin kasa a daidai lokacin da gwamnati take rokon kamfanoni da masana’antu su zo su bunkasa irin wannan kayan abinci da makamantansu.
Da yake yi wa masu ruwa da tsaki bayani a wajen wata ganawa da aka gudanar a harabar kamfanin SDb/SCOA, Kwanturola Bashar Yusuf, ya nemi kamfanoni da masana’antu da ake jiran isowarsu cikin kasa da su lura da muhimman abubuwan da ya kamata su yi amfani da wannan dama wajen gudanar da ayyukansu, ta yadda za su bunkasa harkokin tattalin arziki.
Da yake magana a kan kudin shiga, sai Kwanturola Yusuf ya nuna farin cikinsa da irin nasarar da rundunar ta samu. Ya ce, rundunar kwastam ta Tin-Can ta samu kudi fiye da Naira biliyan 25 da aka tara a cikin watan Nuwamba kadai. Rundunar ta samu tara irin wannan kudi a cikin watan Satumba da ya wuce, a cewarsa.