‘Yan sanda sun cafke wata mota makare da buhunan bushashiyar tabar wiwi a iyakar Jihar Jigawa da makwabciyarta, Kano.
Jami’an da ke sintiri sun kame direban wata mota kirar Fijo dauke da tabar wiwin a kauyen Kijawal da ke Karamar Hukumar Ringim a hanyarsa ta ketarawa zuwa Gezawa a jihar Kano.
Yayin bincike a cikin motar, ‘yan sanda sun gano wasu manyan buhuna cike da ganyen tabar wiwi, wanda a ciki suka samu manyan dauri na busassishiyar tabar wiwi har guda 100.
Kamar yadda bayanai suka nuna, direban motar ya ce an dauke shi haya ne a kan ya kai kayan Gezawa.
A lokacin da ‘yan sanda suke masa tanbayoyin direban motar ya ce wanda ya aike shin da wanda za a kai wa, duk sun tsere bayan samun labarin kama shi.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda na Jihar Jigawa SP Audu Jinjiri ya ce an mika direban ga Sashen Binciken Rundunar da ke garin Kaya domin kammala bincike sannan su mika shi Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin daukar matakin da ya dace.