Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wani boka da mabiyansa da ake zargi da kashe wata Sufeton ‘Yan sanda mai suna Felicia Nwagbara shekaru biyar da suka gabata.
Kakakin rundunar na Imo Micheal Abbatam ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa tun a shekara ta 2017 ne jami’ar ta yi batan dabo.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wanda ya kai kudin fansar basarake a Kano
- ‘Ina da basira da jajircewa, ku taimaka ku zabe ni’
Ya kuma ce mabiyan bokan da aka kama a garin Agwa da ke Karamar Hukumar Oguta ana zargin ’yan kungiyar nan ta IPOB ne masu rajin kafa kasar Biyafara.
Abbatam ya ce bayan kashe ’yar sandan sun ci gaba da aiki kafada-da-kafada da masu garkuwa da mutane da masu aikata manyan laifuka suna kai hare-hare a sassa daban-daban na jihar Imo.
Kakakin ya bayar da sunayen mabiyan bokan da suka hada da Casmire Mgbugha mai shekaru 53, da Hycent Chimezie mai shekaru 30, sai Hycent Ifesinachi mai shekaru 26, da Chukwuemeka Wisdom mai shekaru 22, sai kuma Nandike Clifford mai 72.
“Mun samu sahihin bayani cewa wani boka na hada maganin asiri na karfe da bindga ga ’yan kungiyar IPOB da ’yan ta’addan da ke hulda da ita, wanda har ta kai ga kai harin da yayi sanadiyar mutuwar jami’armu da ke Agwa.
“Da misalin karfe 6 ma safiyar ranar 18 ga watan Mayun 2022 ne muka shirya rundunar da ta gano wadanda ake zargin a maboyarsu da ke Ubah Agwa a Karamar Hukumar Oguta da ke Imo, kuma nan da nan muka zagaye gurin muka kamo su,” in ji Abbatam.
Ya kara da cewa rundunar ta samu Mota Kirar Toyota Camry mai lamba AKD73 BF Lagos, da Mesa mai rai, da bindigogi kirar gida, da kuma harsashi 18, da tutar ’yan awaren Biafra, da kayan ’yan sandan margayiyar da suka kashe.
Haka kuma ya ce a yayin da aka titsiye su sun bayyana kashe Inspekta Felicia Nwagbara, wadda matar daya daga cikin wadanda aka kamo din ne wato Casmire Mgbugb.
Kazalika, sun tabbatar da cewa su masu kera bindigogin gargajiya ne su siyar ga masu satar mutane da miyagu.