Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, a yunkurinta na yaki da masu aikata miyagun laifuka, ta sake cafke mutum 245 da laifuka daban-daban a jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai.
- An haramta yin dariya na tsawon kwana 11 a Koriya ta Arewa
- Buhari zai kai ziyarar kwana uku kasar Turkiyya
Dikko, ya ce a samamen da ’yan sanda karkashin Rundunar Kan Ka-Ce-Kwabo ke kaiwa a kwaryar jihar domin kakkabe masu aikata laifuka, sun yi nasarar kama mutum 245 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
Wadanda aka cafke din ana zargin su da aikata fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu, satar motoci, dabanci, da ta’ammali da miyagun kwayoyi da sauransu.
Kazalika kwamishinan ya ce tuni aka mika wasu daga cikinsu gaban kotu don girbar abin da suka aikata.
’Yan sandan sun kuma kubutar da mutum shida da aka yi garkuwa da su.
Haka kuma an samu bindigogi 35, ciki har da AK47, da bindiga mai sarrafa kanta da sauransu.
Sannan an kwato motoci 26, babur masu kafa uku 14, kekuna 19, wukake 92, gora, kwamfuta hudu, wayar salula 54, janareto 50 da sauransu.
Dukkan wadannan ’kayayyaki an kwato su ne daga hannun bata-garin da kuma barayin intanet a jihar, kamar yadda kwamishinan ya bayyana.