✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama barawon sadakar N600,000 da coci ta tara

’Yan sanda sun cafke wani wanda ya sace Naira 600,00 na sadaka da aka tara a coci a Jihar Ekiti. Wanda aka zargin na daga…

’Yan sanda sun cafke wani wanda ya sace Naira 600,00 na sadaka da aka tara a coci a Jihar Ekiti.

Wanda aka zargin na daga cikin wasu mutum 19 da ’yan sanda suka holen su a Ado-Ekiti, babban birnin jihar.

Kakakin ’yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya ce mutumin ya amsa zargin, kuma za a gurfanar da shi gaban kotu da zarar bincike ya kammala.

Ya ce sauran mutane 18 kuma an kama su ne  bisa zargin su da aikata laifukan da suka hada da satar mutane da fashi da makami da shiga kungiyar asiri da kisa da kuma hada baki wajen yin sata.

Abutu ya kara da cewa an kama su ne bayan samun raotanni daga mazauna yankunansu.

Kayayyaki da aka samu a tare da su sun hada da injin ba da wutar lantarki da takalma da tufafi hadi da tsabar kudi.