An bayyana cewa akwai matsaloli da kalubale a batun samar da ’yan sandan jihohi kamar yadda Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya amince da shi kuma yake ganin abu ne da zai kawo ci gaba a kasar nan.
Tsohon Shugaban karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa kuma jigo a Jam’iyyar APC Alhaji Abdullahi Hassan ne ya bayyana haka a yayin tattaunawa da wakilinmu. Ya ce maimakon ’yan sandan jihohi, me zai hana a kara yawan ’yan sanda a kasa da ake da su don gudun son ran gwamnoni, wadanda da yawansu za su iya amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba.
“A nawa ganin, abu ne mai kyau sai dai akwai matsaloli tattare da lamarin. Kafin a aiwatar da shirin, a fahimtar da talaka tsarin don wadansu na ganin gwamnoni na son amfani da su ne don biyan bukatunsu kamar yadda suke yi ga hukumar zabe ta jiha, kuma wannan abin takaici ne,” inji shi.
Da ya juya kan canja jadawalin zabe da ’yan Majalisar Dokoki ta kasa suka yi, ya ce lamarin ba daidai ba ne, akwai lauje cikin nadi. “Jadawalin ba aikinsu ba ne, wajibi ne a bari mai aiki ya yi aikinsa, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta aka ce, to don me za a yi mata katsalanda? In ba saka suke so da mugun zare ba, mu talakawa ba ma goyon bayansu. Me zai hana in aiki suke so su mayar da hankali ga dokar yin kotu ta musamman kan rashawa da shugaba ya aika masu, ba shigo da wata rigima ba?