Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN), reshen Jihar Kano ta kai ‘ya’yanta 300 kara kotu saboda kin biyan bashin da suka karba.
Shugaban Kungiyar, Alhaji Abubakar Haruna Aliyu, ya bayyana haka a tattaunawarsa da ‘yan jarida a Kano.
“Kungiya ta karbo biyan bashin buhun shinkafa 90,000 daga hannun manoma, sai dai dole ne mu dage wajen cigaba da karbowa. Wannan shi ya sa muka kai wasunsu kotu don su biya, mu ci gaba da tallafa wa manoma da masu sarrafa shinkafa a Kano”, inji shi.
Ya ce kuma sun tuntubi lauyoyin da za su taimaka wa RIFAN wajen karbo bashin ta hanyar shari’a.
Aliyu ya ce kungiyar ta karbo sama da buhu 60,000 na shinkafa kuma za ta ci gaba da karbowa domin ganin an yi ci gaba da tallafawa manoman.
Daya daga cikin lauyoyin, Barista Muhammad Aliyu ya ce sun tuntubi manoma 2,500 a kananan hukumomi 15 kan su cika alkawarin yarjejeniniyar su biya bashin da suka karba.
Ya ce “Mun kai sama da mutum 300 kotu, kuma za mu shigar da karar wasu 200 duk saboda rashin biyan bashin”.
Manoman shinkafan da aka kai kara sun hada da wadanda suka ki biyan bashin da suka karba ne a shekarun 2017 da 2018 da kuma 2019.
Idan ba a manta ba, Hukumar kai-koke, da Hukumar hana masu yi wa arziki ta’annati, sun binciki shugabannin kungiyar RIFAN kan Naira billion N10 da kungiyar ta raba wa manoma a shekarar 2018, da niyyar gano matsalolin da suka sa ba a karbo basussukan ba.