✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai daraktan Kannywood Ashiru Nagoma asibiti

Aminiya ta samu labarin an cewa an kai tsohon darakta a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Ashiru Nagoma, bayan da aka yi ta yada bayana…

Aminiya ta samu labarin an cewa an kai tsohon darakta a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Ashiru Nagoma, bayan da aka yi ta yada bayana game da rashin lafiyar da yake ke fama da ita.

Da take tsokaci a kan lamarin, marubuciya Hajiya Fauziyya D. Suleiman ta wallafa cewa, “Alhamdulillah ala kulli halin, bayan amincewa da ’yan uwan Ashiru Nagoma suka yi, an kai shi asibiti yanzu haka.

“Kuma kamar yadda muka yi alkawari In sha’Allah za mu ci gaba da daukar nauyinsa a karkashin gidauniyarmu ta Creative Helping Needy Foundation.

Tun da farko wasu hotunan tsohon daraktan, wadanda suka nuna shi a tagayyare ko aski babu a kansa, sun dauki hankalin jama’a matuka.

Rashin lafiyar Nagoma

Ganin shi a cikin yanayin ya sa aka yi ta maganganu; wasu na cewa yana fama da tabin hankali ne, wasu kuma na cewa kwalliya ce kawai domin daukar shiri, amma wasu suka ce ai shi darakta ne ba jarumi ba.

Masu masaniya game da halin da Ashiru Nagoma ke ciki na rashin lafiya sun yi ta zargin ’yan Kannywood da yin watsi da shi, wasu ma har da kiran suna.

Hakan ya sa Aminiya ta tuntubi wasu jaruman domin tabbatar da hakikanin lamarin.

Akasarin wadanda Aminiya ta zanta da su sun nuna suna da masaniya, amma ba sa son su yi magana.

Abin da ya faru

Kwatsam, sai Hajiya Fauziyya ta wallafa a shafukanta na sada zumunta cewa lallai yana fama da rashin lafiya, inda ta ce matsalar ta dan kwana biyu.

A cewarta, “Su wa ya kamata su taimaka wa Ashiru Nagoma?

“Tun da na shigo yanar gizo yau na ga hotunan Ashiru Nagoma suna yawo na ji babu dadi, don haka na fara neman wanda na sani a Kannywood domin tattaunawa a kan lamarin.

“Abu na farko da aka fara sanar da ni daga abokan sana’arsa shi ne, tun lokacin da ya fara shiga wannan matsalar suka yi yunkurin kai shi asibiti.

“Sai dai a wancan lokacin ’yan uwansa suka [daka] tsalle suka ce ba su amince ba, har suka yi yunkurin kai wadanda suka yi maganar kara, saboda sun ce an yi wa dan uwansu kagen hauka, da kyar aka samu aka kashe maganar.

Hajiya Fauziyya tare da wasu daga cikin wadanda suka kai darakta Ashiru Nagoma asibiti

“Tun daga wancan lokacin kowa ke tsoron kara tunkarar sa da maganar kai shi asibiti, don haka sai dai idan sun hadu da shi su dan ba shi wani abu.

“Da yawansu sun ce har gida suke zuwa su yi hira da shi su ba shi wani abu, amma suna tsoron kara maganar kai shi asibitin har yanzu da jikin ya yi haka,” inji ta.

Fauziyya ta kara da cewa, “Sada Bin Suleiman Usman ya kira ni a kan yaya za mu taimaka wa wannan bawan Allah yanzu, sai na sanar da shi yadda muka yi da wasu abokan sana’arsa.

“Yanzu dai abun da muka yanke shawara da su abokan sana’ar tasa shi ne: za mu nemi yardar ’yan uwansa a rubuce sannan a kai shi asibitin, kamar yadda da yawa daga ’yan Kannywood din suka yi alkawarin in dai ’yan uwansa sun yarda, to za su dauki nauyin kai shi asibiti,” inji ta.

Zuwa yanzu dai ba mu kai ga samun tabbaci daga likitoci game da hakikanin matsalar da tsohon daraktan ke fama da ita ba.

Kazalika ba mu samu jin ta bakin danginsa ba tukuna, amma za mu ci gaba da kokartawa.

Ashiru Nagoma fitaccen darakta ne da ya yi fina-finai da dama a masana’antar Kannywood, inda yake saka manyan jarumai da yawa a fim guda daya.

Daga cikin fina-finan da ya ba da umarni akwai Tutar So, da Tarayya, da Aure da sauransu.