✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kafa kwamitin binciken rushewar ginin jami’a

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano da kle Wudil, ta kafa wani kwamitin kwararu da zai binciko sanadiyyar rushewar wani bene mai hawa uku…

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano da kle Wudil, ta kafa wani kwamitin kwararu da zai binciko sanadiyyar rushewar wani bene mai hawa uku a jami’ar.
Kwamitin mai mambobi 12 ya hada da wakilan kungiyoyin injiniyoyi na kasa da wasu daga cikin magina da sauran kwararru.
Tunda farko da yake rantsar da ’yan kwamitin, Shugaban Jami’ar Farfesa Shehu Alhaji Musa, ya bayyana cewa rugujewar wani bangaren na ginin da ya faru a makarantar da cewa ya yi sanadiyyar jikkata mutum biyar. “Rushewar ginin ta yi sanadiyayar jikkata mutum biyar, hakan ya sa muka gayyato kwararru don su binciko dalilin rushewar. Kuma  za su ba mu shawarwarin da suka kamata don mu yi amfani da su.” Shugaban Kwamitin kwararrun wanda kuma shi ne Sakataren kungiyar Injiniyoyi ta kasa, Injiniya Mansur Ahmad ya ce kwamitin zai yi kokari wajen sauke nauyin da aka dora masa.
Ana sa ran kwamitin zai mika rahoton abin da ya gano na musababbin rushewar ginin nan da mako uku.