Gwamnatin Imo ta kafa kotunan tafi-da-gidanka don hukunta masu karya dokokin kariyar cutar COVID-19 da aka shimfida a Jihar.
Ta kuma umarci jama’ar Jihar da su kiyaye matakan kariyar cutar COVID-19 saboda hadarinta da cutar ke dauke da shi.
- ASUU za ta bude jami’o’i a watan Janairu 2021 —Minista
- Za a kula da lafiyar masu cutar AIDS kyauta a Kano
- Tsohon Ministan Ilimi Farfesa Agada ya rasu
Tana kuma umartar masu wuraren kasuwanci da wuraren taruwar jama’a da daidaikun mutane su tabbatar da bin matakan kariyar cutar.
Sanarwar da Mashawarcin Gwamnan kan Kariya ta musamman, Ugochukwu Nzekwe, ya fitar ta kuma bukaci mutane su ringa sanya safar rufe baki da hanci da wanke hannuwansu da goga man sinadarin tsaftace hannu da kuma bayar da tazara a wuraren taruwar jama’a.
Sannan kuma jama’a su kaurace wa wuraren da aka tara sama da mutane 100.
Har-ila-yau sanarwar ta bawa ma’aikatan umarnin zama a gida daga ranar Talata 22, ga Disamba, 2020, don su gudanar da bukunkuwansu na Kirsimeti da Sabuwar Shekara.