✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kaddamar da shugabannin kungiyar matasan karamar Hukumar Lere na dandalin yanar gizo

An kaddamar da sababbin shugabannin kungiyar ci gaban matasan karamar Hukumar Lere [LELOGYF] da ke Jihar Kaduna na dandalin yanar gizo a shafin sada zumunta…

An kaddamar da sababbin shugabannin kungiyar ci gaban matasan karamar Hukumar Lere [LELOGYF] da ke Jihar Kaduna na dandalin yanar gizo a shafin sada zumunta na facebook, a garin Saminaka.

Da yake jawabi a wajen taron, tsohon kwamishinan ruwa na Jihar Kaduna, Injiniya Sule Aliyu Lere, ya yaba wa matasan kan kafa wannan kungiya.

 “Gaskiyar  magana yanzu kamar yadda kowa ya sani ne, duniya ta koma a tafin hanu ta hanyar amfani da yanar gizo. Nan gaba kadan ko aikin gona sai an yi amfani da wannan tsari na yanar gizo. Don haka mun yi matukar farin ciki ganin cewa matasanmu sun gano mahimmancin dandalin yanar gizo, sun shiga ciki ana damawa da su.” 

Injiniya Sule Aliyu ya yi bayanin cewa akwai hanyoyi da dama da za a iya amfani da dandalin na yanar gizo. Kuma idan mutum yana son ya zama mutumin kirki zai zama, idan mutum yana son ya zama mutumin banza zai iya zama. 

Ya yi kira ga sababbin  shugabannin kungiyar da su  daina barin mutane suna shiga suna maganganun da basu dace ba. Ya ce amma yana da kyau a rika shiga ana sukar shugabanni kan abubuwan da suke yi wadanda basu da ce ba. 

A nasa jawabin, tsohon shugaban kungiyar, Hamisu Abdullahi Lati ya bayyana cewa daga lokacin da aka zabesu a shekarar 2014 zuwa yanzu da suka sauka. Sun sami nasarar canza  sunan kungiyar  daga kungiyar cigaban matasa Saminaka  zuwa kungiyar cigaban matasan karamar hukumar Lere.

Har’ila yau ya ce sun sami nasarar ziyartar gidajen yari a inda suka tallafawa fursunoni da kayayyaki. Haka kuma sun ziyarci asibitocin yankin inda suka bai wa marasa lafiya tallafin jini.

Hakazalika ya ce sun yi allunan nuna alama na sunayen garuruwa da dama a karamar hukumar. 

Shi ma a nasa jawabin, sabon shugaban kungiyar Kwamared Bukhar Kayarda ya bayyana cewa sun kafa kungiyar ne da manufar tallafawa kansu da kansu da kuma wayar da kan matasa kan illolin shaye shayen miyagun kwayoyi da bangar siyasa.

Ya ce wannan kungiya da aka kafa kamar shekara 10 da suka gabata da mutum 12, a dandalin sada zumunta na facebook ya zuwa yanzu suna da membobi sama da mutum dubu 6.

Kwamared Bukhar Kayarda ya yi bayanin cewa yanzu babban abin da za su sanya a gaba shi ne koyawa matasan yankin maza da mata sana’o’in hannu kamar dinki da kafinta da aski da gyaran mota da walda da gyaran mashin da kuma sanya marayu a makarantu da bai wa matasa masu shaye shaye shawarwari kan illolin yin haka. 

 Don haka ya yi kira ga shugabanni da sauran masu hali na wannan karamar Hukuma da su tallafa wa wannan kungiya kan wadannan ayyuka da suka sanya a gaba.