Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin tallafin matasa na biliyan N75 domin sana’o’i (NYIP) daga Babban Bankin Najeriya (CBN).
Ministan Bunkasa Rayuwar Matasa da Wasanni, Sunday Dare, ya ce a karkashin shirin, CBN zai shekara uku yana ba matasa kudaden tallafin bunkasa sana’o’i da zuba jari.
- Tallafin CBN: Hattara da ’yan damfara
- Yau za a fara rajistar tallafin kanana da matsakaitan sana’o’i
Sunday Dare ya ce tuni gwamnati ta umarci CBN ya samar da Naira biliyan 12.5 domin shirin a watannin da suka rage na 2020.
“Muna godiya ga Ministar Kudi kan yadda ta dage wajen ganin an sanya kashi na biyu da za a bayar a kasafin 2021,” inji shi.
“A kokarinmu na ganin matasa sun yi nasara, mun sanya horarwa a cikin shirin tallafin domin tabbatar da ganin sana’o’in matasan da suka samu sun dore.
“Na yi amannar tallafin zai bunkasa ya kai ko’ina ta yadda masu cin gajiyarsa za su biya”, inji shi a yayin kaddamar da shirin.
Ya ci gaba da cewa gwamnati ta amince da shirin ne domin bunkasa sana’o’in matasa da kara musu karfin jari.
Ya ce matasa masu sana’o’i marasa rajista za su samu N25,000, masu jajista kuma za su samu Naira miliyan uku.
A nasa bangaren, Daraktan Kudi na CBN, Philip Yila Yusuf ya bayyana kwarin gwiwa cewa za su biya rancen mai kudin ruwa na kashi biyar.
“Karon farko ke nan da CBN ke hadin gwiwa da ma’iakatar kuma an samu nasara.
“An bi tsarin dimokuradiyya a tallafin, ba sai mun san mutum kafin ya samu ba.
“Matasa za su gabatar da takardar bayanan abun da suke son yi kawai; Bisa alkaluman da muke da su, muna da yakinin za su biya rancen cikin shekara uku”, kamar yadda ya ce.