✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Kaddamar da shirin koyawa matasa sana’o’i a Kaura

A yanzu haka kimanin matasa da suka hada da: maza da mata 30 ne suke kan samun horo na koyon sana’o’i daban-daban a cikin wani…

A yanzu haka kimanin matasa da suka hada da: maza da mata 30 ne suke kan samun horo na koyon sana’o’i daban-daban a cikin wani shiri da karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna ta fara a matakin farko don koyawa matasa sana’o’i don rage adadin marasa aikin yi a yankin.

Kashi na farko da aka diba wadanda za a koya musu ayyukan da suka hada da walda da kuma dinki, za su kwashe wata uku ne kacal yayin samun horon, inda za a raba musu kayan aiki bayan kammalawa.

Yayin da yake jawabi a wajen taron kaddamarwar da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar da ke Kaura, shugaban karamar hukumar, Dakta Katuka Bege Ayuba, ya hori matasan da mayar da hankalinsu wajen koyon ayyukan da suka zo yi don samun abin dogaro da kansu a rayuwa.

Ya ce daukar wannan matakin ya biyo bayan irin damuwar da yake da shi ne kan matasan karamar hukumar da ya sha alwashin bin duk hanyoyin da suka kamata wajen ganin rayuwarsu ta amfana ta samun abin da za su kyautata gobensu da shi.

Yayin da yake maida jawabi a madadin wadanda za su samu horon, daya daga cikin matasan mai suna Ibrahim Alhassan ya ce ba za su yi wasa da wannan damar da suka samu ba domin yin amfani da ita wajen inganta rayuwarsu ba.